Burkina: An yi jana′izar marigayi Salifou Diallo | Labarai | DW | 24.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Burkina: An yi jana'izar marigayi Salifou Diallo

Dubban jama'a ne suka hallara a ranar Alhamis a abirnin Ouagadougou na Burkina Faso wajen jana'izar shugaban majalisar dokokin kasar Salifou Diallo wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar 19 ga watan Augusta.

Salifou Diallo - Präsident des Parlaments in Burkina Faso (Privat)

Marigayi Salifou Diallo shugaban majalisar dokokin kasar Burkina Faso wanda ya rasu a ranar 19 ga watan Augusta 2017

An samu halartar shugabannin kasashe da na gwamnatoci da dama, cikinsu har da Shugaba Issoufou Mahamadou na Jamhuriyar Nijar, da Alpha Conde na kasar Guinea kuma shugaban Tarayyar Afirka, sannan akwai halartar shugabannin majalisun dokoki na kasashe da dama, inda aka yi addu'o'i a filin wasannin motsa jiki na Palai da Sport na Ouagadougou.

Marigayin dai ya kasance fiye da shekaru 30 ana dama wa da shi a harkokin mulkin kasar ta Burkina Faso, ya taba zama Darectan fadar tsohon shugaban kasar Blaise Compaoré, sannan ya rike mukamin minista lokacin mulkin marigayi Thomas Sankara daga 1983 zuwa 1987, kafin ya rike mukammai da dama daga shekara ta 1987, zuwa 2014, Marigayin ya kafa ta shi jam'iyya ta MPP tare da shugaba mai ci yanzu Roch Marc Christian Kaboré da wasu tsaffin membobin gwamnatin da ta shude. Marigayi Salifou Diallo ya zama shugaban majalisar dokokin kasar ta Burkina Faso a watan Disamba na 2015 har ya zuwa lokacin da rai ya yi halinsa yana dan shekaru 60 da haihuwa..