Bunkasa sana'o'in gargajiya a Najeriya
April 5, 2017Kauyen Gidan Gabas a karamar hukumar Minjibir akwai matasa da ma dattawa masu saka irin ta da amma a yanzu tana neman bacewa. Sani Nura matashi ne mai kishin sana’ar sakar. Ya fadi dalilin rashin sha’awar matasa a wannan sana’a.
“Yawanci ma samarin sun iya amma suna dan fita wasu harkokin ne.To ni gada na yi wurin baba na.Babu wani abu day a sani sama das aka.”
Saka ko a yanzu sana’a c eta dogaro da kai saboda da kyau da kuma ingancin kayayyakin da ake saka wa wadda kuma mutane da yawa ke cin abincinsu da ita.
Abin mamaki shi ne a yayin da masu sha’awar kayan saka ke karuwa a dai dai lokacin masu yin ta ke kaurace mata kamar yadda Mal Mustapha ya fada. Yawanci irin rigunan nan masu adon nan za a gani a jikin wasu yarurruka dai wanda yake ba daya ba, ba biyu ba, wadanda suke mu’amala da su duk za a gani a jikinsu. Ko dai wani ka kalla ka ji dadi ka gaya sa sana’ar ka, kai ba ka ma sa ba. Sana’o’I irin su saka da sassaka da ginin yumbu da dukanci suna daga cikin sana’o’in dake burge masu ziyarar bude ido na gida da ma na waje wadanda da yin su ne suka bunkasa wani fannin tattalin arzikin Nigeria.