Bukukuwan tuna harin Westgate a Nairobi | Labarai | DW | 16.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukukuwan tuna harin Westgate a Nairobi

Shekara guda da afkuwan lamarin, Kenya ta kebe mako guda dan tunawa da wadanda suka rasu lokacin harin da aka kai cibiyar kasuwancin West Gate da ke Nairobi.

A yau ne Kenya ta fara bukukuwan cika shekara guda da harin da aka kai cibiyar kasuwancin Westgate da ke Nairobi, inda suke tunawa da mutane 67n da kungiyar al shabab ta dauki alhakin hallaka wa.

A jawabin da ta yi a wani filin da aka mayar kushewar tunawa da mamatan, da ke kusa da gidan tarihin kasar, mai dakin shugaban kasar Margaret Kenyatta ta ce lallai an raunata yankin gabashin Afirka amma kuma wannan ba yana nufin an karya yankin ba ne, ta kuma ce duk da cewa lokaci ne na makoki ga mutane da yawa, lokaci ne kuma na waraka.

Wannan buki ne ya bude mako gudan da aka kebe dan gudanar da bukukuwan, inda aka fara da kallon wani majigi mai sosa rai da aka yi wa taken "Our Nairobi" a Turance, wanda ya kunshi shaida daga wadanda abin ya shafa.

Ranar 21 ga watan Satumba a shekarar 2013 kungiyar alshabab ta kai hari wannan cibiyar kasuwacin da tsakar rana, ya kuma dauki kwanaki kafin aka ceto wadanda harin ya ritsa da su