1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Bukatar yin sulhu da ‘yan aware

June 20, 2019

Sojojin Kamaru da suka ji rauni a rikicin neman ballewa da kuma iyalansu sun roki gwamnatin shugaba Paul Biya ta zauna kan teburin sulhu da 'yan aware na yankin Ingilishi.

https://p.dw.com/p/3KmEQ
Kamerun Präsident Paul Biya Archivbild 30.01.2013
Hoto: Patrick Kovarik/AFP/Getty Images

Elizabeth Etimu wata wadda ta rasa danta mai shekaru 27  wanda dan sanda ne da 'yan awaren yankin Ingilishi na kamaru suka kashe a garin Manfe da ke yankin  kudu maso yammacin kasar, ta yi roko ga shugaba Paul Biya ya duba bukatar zama da ‘yan awaren domin sulhunta takaddamar. Haka ma kawun mamacin mai shekaru 50 da haihuwa, mai suna Bruno Azegue, ya kasance daya daga cikin dakarun gwamnati da suka fafata da ‘yan aware a baya-bayannan, lamarin da ya haddasa rasa rayukan abokan aikinsa guda hudu. Sai dai bayan da ya tsallake rijiya da baya ya shawarci gwamnati da ta gudanar da tattaunawar samar da zaman lafiya da ‘yan ware domin kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu.

Wasu shugabannin 'yan aware na Ambazonia
Wasu shugabannin 'yan aware na AmbazoniaHoto: Privat

Sojoji da ‘yan sanda 32 aka garzaya da su asibitin Yaounde babban buirnin kamarun sakamkon rauni da suka yi a lokacin da suka fafata da masu neman ballewa na yankin Ingilishi. Sannan kuma an tura da dakaru 14 asibitin sojoji na Douala don yi musu magani. Daya daga cikinsu, mai shekaru 34 da haihuwa, Martial Monthe, ya bayyana cewa a karon farko ya ga ‘yan aware na amfani da makamai na zamani lokacin da suka kai musu hari a garin Eyumojock, lamarin da ya hallaka abokan aikinsa da dama.

Magoya bayan shugaba Paul Biya
Magoya bayan shugaban Kamaru Paul BiyaHoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Gwamnatin Kamaru ta dade da fara zargin 'yan kasar da ke da zama a ketare da tallafa wa 'yan aware da kudaden gudanar da hidimomi da kuma sayen makamai. A cikin watanni uku na baya-bayannan, masu rajin raba kamaru gida biyu sun yi amfani da kafofin sada da zumunta na zamani wajen nuna bama-bamai da manyan bindigogi da suka saya kuma suka shigo da su cikin kasar ta barauniyar hanya. Masanin harkokin siyasa kuma malami a jami'ar Ndjamena Nelson Arrey  wanda haifaffen Kamaru ne ya ce ya kamata gwamnatin Biya ta yi la'akari da makamai da 'yan ware suka mallaka kafin ta tunkaresu

Tun dai shekaru ukun da suka gabata ne kamaru ta fara fuskantar rikici a yankinta na Ingilishi sakamakon zargin gwamnatin da suke yi da mayar da su saniyar ware.