Bukatar shawo kan rigingimun Afrika | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 07.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Bukatar shawo kan rigingimun Afrika

Rikicin Boko Haram da na addini a Janhuriyar Afrika ta Tsakiya, na ci gaba da ci wa kasashen duniya tuwo a kwarya, tare da jaddada bukatar tsaurara matakai.

Za mu fara ne da jaridar Berliner Zeitung wadda ta yi tsokaci kan mawuyacin halin da ake ciki a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Jaridar tace a tsakiyar watan faebrairun daya gabata ne dai shugaba Goodluck Jonathan da jami'an tsaron Najeriya suka yi ikirarin kusan samun nasara a yakin da suka yi da kungiyar nan ta fafutuka da ake kira Boko Haram. Sai dai yini guda bayan wannan furuci na shi aka kai hari a kan garin Bama da ke jihar Borno , harin da yayi sanadiyyar rayuka masu dumbin yawa. Kwanaki kalilan bayan nane kuma maharan suka afakawa garin Buni Yadi dake jihar Yobe, inda aka yi wa yaran makarantan kwana ta gwamnatin 59 yankan rago, baya ga wasu da aka yi awaongaba da su. Jaridar ta ce, bayannan ne aka kai harin boma bomai a kan wasu kauyuka guda biyu dake Borno, da kuma cikin garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar, hare haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 116.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama dai sun sha sukan hukumomin tsaron na Najeriya. Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta ce jami'an tsaro na amfani da yaki da kungiyar Boko Haram wajen cin zarafin fararen hula, inda sukan kutsa gidajen mutane da kasuwanni da Masallatai suna kame maza musamman matasa.

Ita kuwa jaridar Der Tagesspiegel cewa ta yi, bayan shekaru 110 Jamus ta mika sauran kasusuwan gwaran Namibiya da aka yi wa kisan kiyashi. Ministan al'adu na Nabiya Jerry Ekandjo shi ne ya karbi wadannan kasusuwa. Wadannan kasusuwa na tarihi dai sun kasance ne a wani asibitin ajiyan kayayyakin tarihi da ake kira der Charite. A ranar talatar nan ce dai ministan Namibiyan ya karbi kasusuwan kwakwalwar mutane 14 daga asibitin Freiburg. Idan za'a iya tunawa dai a shekara 2011 ne Jamus din ta fara gabatarwa da Nabiyan kasusuwan mutane 20. Akan bayyana Kasar dai da kasancewa "Jamus ta kudancin Afrika". Saboda mulkin mallaka da Jamus din ta yi mata daga shekara ta 1884 zuwa 1915.

Bari mu sake komawa ga jaridar Berliner Zeitung wadda a cewarta halin da ake ciki a Janhuriyar Afrika ta Tsakiya na dada tayar da hankulan kasashen duniya. Kawo yanzu dai mutane 2,000 ne suka rasa rayukansu, a yayin da wasu miliyan guda sun tsere domin neman mafaka, a wannan kasa dake da yawan al'umma miliyan biyar. A yanzu haka dai ana muradin kasancewar sojojin kiyaye zaman lafiya na hadaka dubu 12. Wanda hakan ba zai isa biyan bukatar da ake so na kare fararen huluar kasar daga hare haren mayakan Christoci da na Musulimi ba, kamar yadda sakatare janar na MDD Ban ki-Moon ya sanar wa komitin sulhu ba a wannan Litinin.

A yanzu haka dai Tarayyar Afrika na da sojoji 6,000, a yayin da Faransa ke da 2,000 kana Tarayyar Turai za ta bada gudunmowar 1,000. A wannan Larabar ce dai za'a tantance kasashen da za su bayar da gudunmowar sojoji da kuma adadinsu. A yanzu haka dai Tarayyar Jamus nada jiragen sama dake ayyukan samar da magunguna da kiwon lafiya, kama daga headkwatar sojojin Turai dake Girka, zuwa birinin Bangui dake zama fadar gwamnatin janhuriya Afrika ta tsakiya.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Nasir Awal