Bukatar magance matsalar yunwa | Labarai | DW | 12.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukatar magance matsalar yunwa

Hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce hanya daya tilo ta magance karancin abinci a duniya, ita ce ta kawo karshen rikice-rikice.

Wani babban jami'in hukumar David Beasley ne ya bayyana hakan, yayin ganawar da ya yi da kamfanin dillancin labaran Amirka AP cikin wannan makon. A cewarsa baya ga inganta samuwar abincin zaman lafiya zai kuma ceto bliyoyin dalolin da ake asararsu, inda ake iya amfani da su wajen gudanar da wasu muhimman aikace-aikace a kananan kasashe. Ya bayyana matukar takaicinsa kan yawan kudaden da hukumar ke kashewa a yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula.

Alkaluman baya-bayan nan dai sun yi nunin da cewa mutane miliyan 815 ne ke fama da yunwa a duniya, kuma galibinsu daga kasashen da ke fama da rikici. Kasashen da wannan matsala ta fi muni dai sun hada da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da Sudan ta Kudu da Siriya da Yemen da Somaliya da kuma Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango.