Ghana: Bukatar ladaftar da minista
July 22, 2020Bukatar gurfanar da ministar kana 'yar majalisa da ke wakiltar jam'iyyar NPP a mazabar Ewutu Senya ta gabas a gaban kwamitin ladabtarwar na majalisar dokoki dai, ya biyo bayan harba bindiga sau hudu da ta yi a wani dandali da ake gudanar da atisayen rarraba katin zabe kana cikin cincirindon jama'a. Harbe-harben dai ya janyo an kame matasa hudu bisa zarginsu da aikata laifin harbi da kuma kona babura na ma'aikata, sai dai daga bisani ministar ta fito karara tana mai cewa: Babu wani mai makami a wajen, da kaina na harba bindigar domin gargadi, ko kuma ana so a nuna min cewar ba zan iya kare kaina ba ne?"
Majalisar wanzar da zaman lafiya ta Ghana tayi Allah wadai da wannan al'amari ta bakin shugabanta Rev. Emmanuel Asante. Duk da haka dai bangaren gwamnati da ke da rinjaye a majalisar dokokin kasar, ya wofintar tare da bayyana kiraye-kirayen da bukatar shugaban kasa ya tisge ministar ko kuma ta yi murabus da kanta, a matsayin wani abu da ba shi da tushe balle makama.
Duk wani kokari na jin ta bakin gwamnatin da DW ta yi ya ci tura. Kwararru a kan harkokin tsaro sun nuna damuwarsu kan yadda rashin jure hamayyar siyasa daga jami'an gwamnati a Ghana ya kai kololuwa, musamman a yayin da zaben shugaban kasar ya rage kasa da watanni biyar. Abin jira a gani shi ne yadda doka za ta hukunta ko kuma kare ministar.