Bukatar kudade don yaki da yunwa | Labarai | DW | 23.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukatar kudade don yaki da yunwa

Majalisar Dinkin Duniya na bukatar miliyoyin daloli don maganta matsalar abinci cikin kasashe hudu.

Guterres UN PK zu Hungersnöte in Afrika (picture-alliance/Zumapress/A. Lohr-Jones)

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteres, ya yi kiran gaggawa na hadin kan kasashen duniya don samun akalla dala biliyan hudu da rabi da a yi amfani da su wajen ceto kasashen da ke fuskantar hadarin yunwa a bana. Kasashen da matsalar za ta shafa dai su ne kasar Sudan ta Kudu da Najeriya da Somalia da kuma kasar Yemen. Sakataren na Majalisar Dinkin Duniyar Mr. Guteres ya ce dala miliyan 90 ne ke a hannu ya zuwa yanzu, lamarin da kuma ke bukatar tallafi cikin hanzari.

Hasashe ya yi nunin cewa sama da mutane miliyan 20 ne za su fuskanci matsalar abinci a watanni 6 nan gaba, lamarin ma da tuni aka soma ganinsa a kasar Sudan ta Kudu. Kalaman Mr. Guteres dai sun yi nunin cewa wasu jami'an MDD da kungiyoyin agaji ma sun riga sun nuna manyan alamun faruwar wannan matsala a kasashen 4.