Bukatar kotu ta saki Julian Assange nan take | Labarai | DW | 01.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukatar kotu ta saki Julian Assange nan take

Kwanaki kalilan gabanin yanke hukuncin iza keyar dan jaridar nan Julian Assange zuwa Amirka, kungiyar 'Yan Jaridu na Gari na Kowa, ta yi kira da a saki wanda ya samar da kamfanin kwarmato na Wikileaks nan take.

DW Dokumentationen WikiLeaks - Staatsfeind Julian Assange

Julian Assange wanda ya samar da kamfanin kwarmata bayanai na Wikileaks

Acewar manajan kungiyar ta 'Yan Jaridu na Gari na Kowa, zargin da Amirka ke yi wa Assange na da alaka da siyasa ne kawai. Amirka dai na son bayar da misali ne wajen yankewa dan jaridar hukunci. A ranar Litinin mai zuwa hudu ga wannan wata na Janairu da muke ciki ne dai, wata kotu a birnin London na kasar Birtaniya za ta yanke hukuncin mika shi zuwa Amirkan.