Bukatar gurfanar da wadanda suka mika wuya | Siyasa | DW | 16.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bukatar gurfanar da wadanda suka mika wuya

'Yan Najeriya sun nemi jami’an tsaro da gwamnati da su kiyaye hakkokin wadanda jami’an tsaro suka bayyana nema ruwa a jallo kuma suka mika wuya domin gudanar da bincke.


A wannan Litinin din ce dai biyu daga cikin wadanda ake nema wato Aisha Wakil da ake kira Mama Boko Haram ta mika kai ga jami'an tsaro da ke Abuja inda lauya Ahmed Bolori ya mika kansa ga rundunar tsaro ta bakwai mai cibiya a Maiduguri.Na ukun su wanda dan jarida Ahmed Salkida wanda yanzu haka baya kasar shi ma ya fitar da sanarwar cewa yana hanyar zuwa don amsa duk wata tuhuma da za'a masa inda ya nemi jami'an tsaron su aike masa da tikitin jirgi don ya gaggauata zuwa.


Kungiyoyin fararen hulan dai sun nemi a gaggauta gabatar da su gaban kuliya maimakon tsaresu na tsawon lokaci da sunan bincike ko kuma muzguna musu da sunan tatsar bayanai.Suma talakawan kasar da masharhanta sun nemi jami'an tsaro da kar su ci zarafin su wadan nan bayin Allah tunda tuhumar su ake yi inda kuma suka nemi a tabbatar musu da dukkanin hakkokin su da doka ta tanadar.Shi kuma Hon Adamu Musa Dan Amar cewa ya yi, mika wuya da wadanda ake neman suka yi ya nuna cewa yanzu Najeriya ta samu chanjin da ta ke nema saboda doka da oda ya dawo kasar kuma wadanda ake zargin sun san za'a musu adalici shi ya suka mika wuya.

Sauti da bidiyo akan labarin