Buhari ya umarci a kamo hafsoshin tsaro | Siyasa | DW | 18.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Buhari ya umarci a kamo hafsoshin tsaro

Daga cikin mutanen da aka bada umarnin kamawa harda Sambo Dasuki da sauran manyan jami'an tsaro wadanda ake tuhuma da hannu a wawure kudin sayen makamai

A wani abun dake zaman badakalar mafi girma a cikin duk wani yaki da Tarrayar Najeriya ta jagoranta, wasu manyan hafsoshin tsaro da jami'an yakin na shirin fuskantar kuliya sakamakon wakaci ka tashi da dukiyar kasar da sunan yaki.
Sama da Naira miliyan dubu 643 ake batu, bayan wasu daloli na Amurka miliyan dubu biyu, duk sun shiga shannun sarki a cikin yakin ta'addancin kasar na shekaru shida .

Kuma manyan jami'ai na yakin da suka hada da hafsoshin sojan kasar game da shi kansa mai bada shawara ga harkar ta tsaro ne dai, wani kwamitin sirri na gwamnatin kasar ya bankado , sannan kuma shugaban kasar yace a cafko su domin gurfanar dasu ga shari'a.

Duk da cewar dai mahukuntan na Abuja sun ki fadar sunayen a bisa tsoron yiwuwar rantawarsu cikin na kare, babban laifinsu a cewar sanarwar fadar na zaman ko dai kai kudin ga wasu kamfanonin da suka karba, amma suka ki aiwatar da kwangilolin samar da makaman yakin, ko kuma karkatar da kudaden ba hujja.

Akalla jiragen yaki 10 ne dai aka karbi kudin gwamnatin amma ba keyarsu, banda ragowar makamai iri- iri na yakin ga sojan kasar, da ke da tarihin yaki amma suka kalli kadangare a bakin tulunsu. Ko wane lokaci daga yanzu dai ana shirin ganin kame ga jami'an da abaya suke fadi ana amsawa, amma suke shirin shiga yar buya a cikin tsoro.

Tuni dai an shiga nunin yatsa a tsakanin tsohon mai bada shawarar Sambo Dasuki da yace ba'a gayyace shi gaban kwamitin domin jin ba'a sin ba, da kuma fadar gwamnatin kasar da ke fadin zuki tamalle ce, a fadar Mallam Garba Shehu dake zaman kakakin shugaban kasar.

To sai dai koma ya zuwa yaushe ne jami'an tsaron ke shirin fara aikin kame na tsofaffin masu gidan nasu da sunan hancin yakin na ta'adda dai, tuni muhawara ta dau dumi cikin kasar dake kallon satar da ta wuce hankali ga kasar dake fuskantar yaki amma kuma ke fuskantar manyan beraye a cikin rumbun yakin.

Sauti da bidiyo akan labarin