Buhari ya kaddamar da rundunar yaki da satar shanu | Siyasa | DW | 13.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Buhari ya kaddamar da rundunar yaki da satar shanu

Barayin shanu da 'yan fashi na jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya za su gamu da fishin soji daga yanzu idan suka sake aikata ta'asa, lamarin da ke zama kalubale ga rundunar kasar da ke yakar Boko Haram.

Saurari sauti 03:31
Now live
mintuna 03:31

Hira da wakilinmu Mohammed Abba kan kafa rundunar yaki da barayin shanu

Sace-sacen shanu a yankin Arewa maso yammacin Najeriya sun kai ga kashe Fulani makiyaya a shekarun baya-bayannan. Saboda haka ne a shekara ta 2015 gwamnonin wannan yanki suka kafa rundunar hadin gwiwa ta jami'an tsaro, wadda aka dora wa nauyin shiga dajin da barayin shanu ke aikata munanan ayyuka don ja musu birki.

Sai dai al'ummar Arewa maso Yammacin Najeriya sun ta korafi kan wannan runduna, inda suka ce ba shi da tasirin a zo a gani saboda ana ci gaba da zubar da jini.

Saboda haka ne gwamnatin tarayya ta shiga cikin harkar, inda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da rundunar sojoji ta musamman domin yaki da barayin shanun.

Ministan Tsaro Mansur Dan Ali, ya ce akalla dakarun sojojii dubu ne za a tura a yanzu haka. Sai dai za a kara adadinsu daga bisani. Wannan lamari dai ya zo ne a daidai lokacin da jami'an tsaron Najeriya ke yaki da Boko Haram, lamarin da ke zame musu wani sabon kalubale.

Sauti da bidiyo akan labarin