Buhari: Mun samu tallafin Bankin Duniya | Labarai | DW | 21.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari: Mun samu tallafin Bankin Duniya

Wannan bayani na zuwa ne bayan da shugaba Buhari ya gana da wakilan Bankin Duniya da gidauniyar Bill and Melinda Gates da ma wakilan Hukumar Lafiya ta Duniya.

Niger Buhari Issoufou

Shugaba Buhari na Najeriya

Fadar shugaban Najeriya ta bayyana a ranar Talatan cewar Bankin Duniya ya yi alkawarin kashe sama da Dala miliyan dubu biyu wajen sake gina Arewacin Najeriya da ayyukan ta'addancin Boko Haram ya daidaita.

Wannan kungiya dai ta masu tada kayar baya da ayyukanta na tsawon shekaru shida sun dagula lamura a yankin da suke ikirarin neman kafa daular Islama.

Wannan jawabi na zuwa ne bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya gana da wakilan babban Bankin na Duniya da gidauniyar Bill and Melinda Gates da ma wakilan Hukumar Lafiya ta Duniya a lokacin ziyarar da ya kai birnin Washington na Amirka.