Buhari: Kasafin fatan aiwatar da sauyi a Najeriya | Siyasa | DW | 22.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Buhari: Kasafin fatan aiwatar da sauyi a Najeriya

A wani mataki da ake ganin na fara aiwatar da sauyi a Najeriya, shugaban Najeriyar ya gabatar da kasafin kudin gwamnatinsa na farko na Triliyan shida da miliyan 80.

Sabon kasafin da ke zaman irinsa mafi girma a tarihi na kasar dai na kunshe da Naira Triliyan daya da miliyan dubu dari takwas ko kuma kaso 30 a cikin dari na daukacin kasafin domin manya na aiyyukan raya kasa.

A cikin adadin manyan aiyyukan da gwamnatin kasar take shirin yi a badin dai ma'áikatar hasken wutar lantarki da aiyyuka da gidaje ce ta tashi da kasafi mafi tsoka na Naira Billiyan 433 a yayin kuma da yar uwarta ta sufuri zata gudanar da muhimman aiyyuka na Bnaira Billiyan dari biyu da biyu. Maáikatar tsaron kasar ta samu Naira biliyan 134 a yayin kuma yar uwarta ta cikin gida ta samu biliyan 51 duk domin manya na aiyyuka a shekarar dake tafe.

A badin dai har'ila yau Tarrayar Najeriyar na shirin batar da tsabar kudi har Triliyan 2 da miliyan dubu 590 domin biyan albashi da saura na aiyyukan yanzu da an jima. Adadin kuma a cikin maáikatar ilimi ta tashi da kaso mafi tsoka na naira Biliyan 369. sai maáikatar tsaro da zata samu Naira Biliyan 294 sai kuma harkoki na lafiyar da za sau lamushe Biliyan 221.

National Assembly in Abuja, Nigeria

Kasafin na badi dai a fadar shugaban kasar na da buri na sake farfado da tattalin arzikin kasar dama samar da aiyyukan yi ga matasa.Alal misali dai a fadar shugaba Buharin gwamnatin kasar zata hada kai da jihohi da kananan hukumomi domin daukar malaman makaranta 500,000 da zaá kaisu ga makarantu na firamare na kasar da nufin habaka ginshikin ilimi na kasar.

"A wani abun da ke zaman matakin gaggawa da nufin rage karancin malamai a makarantu na gwamnati, zamu hada kai da jihohi da kananan hukumomi da nufin dauka tare da horar da masu takardar shaidar digiri da kuma shaidar koyarwar ta NCE 500,000 . Wadannan zasu yi aikin koyarwa a makarantu na firamarenmu da nufin sake ginin ginshikin ilimi na kasarmu".

Wani batu da har ila yau ya dauki a hankali a jawabin na kusan mintuna 30 na zaman yakin kasar na cin hanci da shugaban ya ce zai cigaba har sai an tabbatar da kwato kowane sisin satar da ke ciki dama wajen kasar a halin yanzu.

"Zamu kwato daukacin dukiya ta 'yan kasar da aka sace. Ko a ína aka kaita domin buya kuma komai nisa na lokaci".

Duk da cewar dai kasafin ya sha tafi a gaban 'yan dokar da ke sauraren Buharin a karon farko a cikin zauren majalisar, babban kalubale daga dukkan alamun na zaman hanyoyin samar da kudin da tun ba á kai ga koína ba ke fuskantar kalubale mai girma..

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria

Majalisar Najeriya

Alal misali dai a yayin kasafin ke dore a kan dalar Amurka 38 kowace gangar man fetur, tuni bakar hajjar tai nitso zuwa dala 32 da safiyar yau din nan.

Abun da ke nuna alamun girman gibin kasafin da tun da farko ya karkata ga harajin da babu shi har yanzu maimakon man fetur din dake zaman madogarar aláda.

Kasar ta Najeriya dai na fatan ranto kusan daya a cikin ukun kudaden na batarwa daga ciki dama wajen kasar domin biyan bukatar ta badi.

To sai dai kuma sauki ga 'yan kasar na zaman aniyar gwamnatin ta kyale farashin man fetur kan naira 87 ya zuwa yanzu abun da ke nuna alamar tallafi zai zarce duk da babu dalla dalla ta yawansa zuwa yanzu

"Na umarci hukumar tsara farashin man fetur da dangoginsa ta PPRA da ta sake nazarin tsari na farashin hajjar domin da cewa da zahiri na kasuwa. Muna fatan hakan zai rage kudaden da ake kashewa a cikin wannan harka tare da samun rarar ta yanda man fetur zai cigaba da kasancewa kan naira 87 kowace lita ya zuwa yanzu".

Abun jira a gani dai na zaman iya kaiwa ga cikon alkawuran da ke cikin kasafin da ke nunin alkiblar saukaka rayuwar alúmmar dake zaman fifiko a zuciya ta gwamnatin.

Sauti da bidiyo akan labarin