Buhari: Birtaniya ta maido da kaddarorinmu | Labarai | DW | 11.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari: Birtaniya ta maido da kaddarorinmu

Shugaban ya ce baya bukatar afuwa daga wajen fraiministan Britaniya dangane da zargin Najeriyar na zama kan gaba a cin hanci.

Buhari ya ce abIn da ke da muhimmanci shi ne BIRtaniya ta mayar da satattun kaddarorin jami'an kasar da ke samun mafaki a london.

Ya ce "abIn da na ke muradi kawai shi ne, Britaniya ta mayar da kaddarori da aka sace a Najeriya aka boye a can. Na riga na yi bayanin yadda BIRtaniya ta ke jagoranci, da kuma irin abun kunya da wani babban jami'in Najeriyar ya yi, na ba da kamanni a tufafin mata domin gudu daga Birtaniya, inda ya bar kaddarorinsa da irin dumbin kudaden da ya jibge a bankuna, wanda kuma ake shirin mayar mana da su, irin abin da nake tambaya kenan".

Shugaban najeriyar ya yi wannan tsokaci ne a wani dandalin mahawara da aka shirya kan yaki da rashawa a sakatariyar Kungiyar Common Wealth da ke birnin London. Ya na misali ne da tsohon gwamnan Bayelsa mai arzikin mai Alamieyeseigha, wanda aka tsare a london a shekarata 2005.

A gobe Alhamis ne dai David Cameron ke karbar bakunci shugabannin kasashen duniya a taron yaki da cin hanci da rashawa, ciki har da Buhari da Ashraf Ghani na Afganisatan, kasashe biyun da ya bayyana da kasancewa a gaba wajen cin hanci.