1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Buhari ya ce ya cika alkawuransa

January 21, 2019

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kaddamar da gangamin yakin neman zaben shugaban kasa a jihohin Borno da Yobe wanda ya samu halartar jiga-jigan jam’iyyar karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

https://p.dw.com/p/3BvNw
Nigeria Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: picture alliance/AP Photo/S. Alamba

Yakin neman zaben na zuwa ne a yayin da jihohn Borno da Yobe da ke fama da matsalar tsaro inda bangarorin Boko Haram ke zafafa hare-hare tare da su ka yi sanadiyyar hallaka sojojin Najeriya a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ayarin yakin neman zaben Shugaban Muhammadu Buhari ya sauka a Maiduguri da safiyar Litinin inda bayan kai ziyarar ban girma ga Shehun Borno ya zarce zuwa filin sukuwa domin yin jawabi ga cincirindon magoya baya da suka yi sammako domin ganin shugaban da kuma saurarar bayanai da zai yi.

Nigeria Militär Präsident Muhammadu Buhari
Buhari dai ya ce ya yi rawar gani ta fuskar tsaro a BornoHoto: NPR

A jawabinsa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi bitar alkawuran da ya yi a lokacin neman a zabe shi wanda suka hada da samar da zaman lafiya da gyara tattalin arzkin kasa gami da yaki da cin hanci wanda ya ce ya cika wadan nan alkawura.

Sauran mukarraban jam'iyyar da su ka yi jawabai sun yi amfani da damar gangamin yakin neman zaben wajen maida martani ga wasikar tshohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo wanda ya caccaki gwamnatin Shugaba Buhari kan rashin tabuka komai musamman a fannoni  tsaro da tattalin arzikin kasa.

Wannan dai shi ne karo na hudu da shugaban na Najeriya ya taka jihar Borno tun bayan da ya dare kujerar mulkin Najeriya a shekara ta 2015. An dai gudanar da wannan yakin neman zabe a Maiduguri jihar Borno da Damaturu hedikwatar jihar Yobe lami lafiya ba tare da samun wata matsala ta tsaro ba.