Bude gasar kwallon kafa na Afirka | Labarai | DW | 14.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bude gasar kwallon kafa na Afirka

An bude gasar neman cin kofin kwalon kafa na Afirka wanda Gabon ta dauki nauyi kuma za a shafe kwanaki ana fafatawa domin tantance gwani.

A wannan Asabar aka bude gasar neman cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afirka da kasar Gabon ta dauki nauyi, inda kasashe 16 na nahiyar da suka samu damar zuwa gasar za su fafata cikin kwanaki masu zuwa domin tantance zakaran kasashen na wannan karo.

Mai masaukin baki Gabon tana fafatawa da kasar Guinea Bissau, wanda ke zama wasan farko cikin gasar.

A wani labarin ministan kula da wasanni na Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango, Willy Bakonga yana cikin wadanda suka halarci gasar domin warware yajin aikin da 'yan wasan kasar suka fara kan rashin biyansu kudaden da suka dace na alawus.