Brexit: Wasu ′yan Birtaniya sun damu | Siyasa | DW | 19.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Brexit: Wasu 'yan Birtaniya sun damu

Shekara guda da kuri'ar ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai, 'yan Birtaniya na nuna takaici dangane da rashin ci gaba da kuma makoma ta gari da kasarsu ke fuskanta. Akwai ma masu hangen rincabewar lamaura a tattaunawar.

Zaben raba gardama da aka gudanar ranar 23 ga watan Yunin bara ya haifar da sauyi a fagen siyasar kasar ta Birtaniya, saboda ya kai ga fitar da Firaministan wancan lokaci David Cameron. Sannan Theresa May da ta gaje shi ta sha kaye a zaben gaba da wa'adi da ta shirya, duk da cewa ta shigar da bukatar janye kasarta daga Kungiyar Tarayyar Turai kamar yadda doka mai lamba 50 na EU ta tanada. Sai dai duk da hakan, 'yan Birtaniya sun kasa sanin inda aka kwana game da ficewa daga Turai, a cewar Matthew Cole, malamin tarihi a jami'ar Birmingham da ke kasar.

"Brexit, an fara dakatar da shi da farko saboda wasu jerin zabubbuka. Sannan kuma aka  jinkirta shi sakamakon muhawara da aka tafka kan hanyar da kasar Birtaniya ta kamata ta bi wajen fita daga EU. Theresa May ta yi kokarin bayyana alkiblar da za a dosa a watan Janairu, inda ta ce Birtaniya za ta fita kwata-kwata daga kasuwar bai daya ta Turai,  tare da yin watsi da tsarin EU na fito. Sannan Birtaniya ta samar da tsarinta na shige da fice. Amma kuma babban zabe da aka gudanar ya sake farfado da muhawara kan wannan batu"

Shekaru biyu Birtaniya da sauran kasashe mambobin Eu za su shafe suna tattaunawa tsakaninsu don cimma matsaya kan hanyoyin raba gari, walau cikin ruwan sanyi ko kuma a tashi baram-baram. Sai dai ana ci gaba da samun rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan Birtaniya kan wannan batu. A zaben raba gardamar dai, kashi 52 a cikin 100 ne suka yi na'am da ficewa daga EU, yayin da kashi 48 bisa dari suka nuna bukatar ci gaba da kasancewa cikin kungiyar tarayyar Turan. Oliver Zanetti, da ke gudanar da bincike a jami'a, ya ce shekara guda bayan zaben na raba gardama, har yanzu 'yan Birtaniya sun kasa gane amfanin ficewa daga EU.

"Ba na zaton ra'ayi ne ya canza tun bayan gudanar da zabe; ina dai ganin cewar ficewa ba abu ne mai kyau ba. Har yanzu babu wanda ya gabatar da kwararan dalilin da suka kamata mu dogara a kai wajen ci gaba da mutunta matakin ficewa daga EU. Ba wanda yake da karfin zuciyar bayan cewar hanyar da muka dauka ba mai kyau ba ce. Muna ci gaba da jajircewa kan Brexit ne, saboda babu wanda zai ja mana birki. Wannan abin takaici ne."

Ko da yake kashi 48 daga cikin 100 sun zabi ci gaba kasance a cikin kungiyar ta EU, kididdigar jin ra'ayin jama'a ta nunar da cewa mafi yawan 'yan Birtaniya sun nuna bukatar gwamnati ta ci gaba da matakin ficewa daga kungiyar.Batun na Brexit dai bai taka rawa ba a zaben 'yan majalisa da aka gudanar a farkon wannan wata na Juni. Maimakon haka, batutuwa na jin dadin rayuwa da kuma hare-haren ta'addanci da Birtaniya ke fama da su ne suka sa Firaminista Theresa May, rasa rinjayen da take da shi a majalisar dokoki.