1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brexit: Majalisa ta sake watsi da shirin May

March 29, 2019

Siyasar Birtaniya na shirin dagulewa bayan watsi da bukatar da firaministar kasar ta gabatar wa majalisa dangane da ficewa daga kungiyar EU.

https://p.dw.com/p/3Fuds
Großbritannien London - Debatte zum Brexit
Hoto: picture-alliance/dpa/PA Wire/House of Commons

A karo na uku a jere 'yan majalisar dokokin Birtaniya sun sake yin fatali da shirin ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai da firaminista Theresa ta gabatar masu.

Matakin majalisar ya sake dagula yiwuwa ko ma daukacin shirin ficewar daga gungun kasashen na EU.

Theresa May, ta ce ''wannan majalisa ta yi watsi da fita ba tare da yarjejeniya ba, sannan ta yi fatali da soke shirin ficewar baki daya, kana a ranar Laraba majalisa ta sake sa kafa ta shure dukkan nau'oin shawarwari da aka gabatar, a yau kuma ta sake kin amincewa da yarjejeniyar ficewa da za ta bamu damar tattauna makomar dangantakarmu a gaba''.

Theresa May dai ta kekashe kasa tana mai cewa gwamnatinta za ta ci gaba da matsa kaimi kan shirin ficewa daga EU cikin lumana kamar yadda sakamakon kuri'ar raba gardamar da 'yan kasa suka kada ya bukata.

Watsi da daftarin na Theresa May dai na nufin ya zama wajibi kasar ta sake gabatar wa kungiyar tarayyar Turai wani tsarin jadawali ko kuma ta fice a ranar 12 ga watan Afrilu ba tare da cimma wata yarjejeniya ko madafa ba.