1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brexit: Jakadun EU sun tattauna cinikayya

December 25, 2020

Wakilan kasashen kungiyar EU sun gana domin nazarin daftarin yarjejeniyar cinikayyar da suka cimma da Birtaniya kafin mika daftarin ga majalisar dokokin Turai domin amincewa

https://p.dw.com/p/3nDy5
EU Brexit | Michel Barnier
Hoto: Olivier Hoslet/AP Photo/picture alliance

Jakadu daga kasashen 27 na kungiyar tarayyar Turai sun gana a yau kirismeti don fara tantance yarjejeniyar cinikayya mara shinge da kungiyar ta kulla da tsohuwar mambarta Birtaniya yarjejeniyar dake zama babban abin tarihi.

A taron na mussaman, wakilan EU sun bukaci karin lokaci don yin nazari kafin turawa ga 'yan majalisar tarayyar Turai kuma ake sa ran jakadun su kara ganawa a ranar Litinin mai zuwa a cewar wani jami'in diflomasiyyar kungiyar.

Firanminsitan Birtaniya Boris Johnson ya yabawa yarjejeniya inda ya baiyanata a matsayin matakin farko na alakar danganta tsakanin Birtaniyar da makwaftanta na tarayyar Turai.

An dai cimma matsayar cewa karkashin yarjejeniyar babu kudin fito ko kayyade cinikayya a tsakanin bangarorin biyu.