SiyasaTurai
Brexit: Shugaban kungiyar EU ya soki Birtaniya
September 26, 2020Talla
A yayin da yake magana a sakonsa na bidiyo ga taron Majalisar Dinkin Duniya Mr. Michel ya yi shagube, inda ya ce a zamanin da muke ciki kiri-kiri wasu na amfani da karfin gwamnati fiye da kima, akwai kuma wasu da ke saba yarjejeniyar da suka rattaba hannu a kanta.
Masu sharhi dai sun yi ittifakin cewa wannan wani babban sako ne zuwa ga hukumomin Birtaniya cewa EU ba ta goyon bayan shirin kawo sauyi a yarjejeniyar Brexit da ta ba Birtaniya damar ficewa daga Tarayyar ta Turai.