1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brexit: EU ta ce bakin alkalami ya bushe

February 4, 2019

Kungiyar EU ta ce babu wani abin da ya saura wa Birtaniya kan duk wata yarjejeniya da aka sanya wa hannu a baya.

https://p.dw.com/p/3ChxG
Jean Claude Juncker und Michel Barnier
Hoto: Reuters/F. Lenoir

Tarayyar Turai ta ce ba za ta sake waiwayen yarjejeniyar ficewar Birtaniya daga gamayyar kasashen kungiyar ba, ciki har da matsayin yankin nan na Ireland mai sarkakiya.

Sai dai babban mai shiga tsakani kan batun ficewar Birtaniyar daga kungiyar Michel Barnier wanda ya sanar da a wannan Litinin, ya ce akwai yiwuwar samun mafita kan batun ficewar kasar.

A ranar 29 ga watan gobe ne dai Birtaniyar za ta fice daga kungiyar, koda yake majalisar dokokin kasar ba ta amince da batun iyakar Ireland ta Arewa da jamhuriyar Ireland ba.

Matsalar dai ita ce batun shige-da-fice a iyakar Jamhuriyar Ireland wadda za ta ci gaba da zamanta cikin kasashen Turan, yayin da Ireland ta Arewa ke cikin Birtaniya.