1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brexit: Theresa May na kokarin shawo kan 'yan majalisa

Ramatu Garba Baba
January 28, 2019

Theresa May ta shiga neman sabuwar hanyar fitar da kasar daga Kungiyar Tarrayar Turai EU, bayan da ta nemi amincewar 'yan Majalisa a kan batun na Brexit yayin da ake ganin lokaci na neman kure mata.

https://p.dw.com/p/3CKDP
Großbritannien House of Commons in London | Theresa May, Premierministerin
Hoto: picture-alliance/House of Commons/empics

Kakakin Firaiministar, ya sanar da cewa,  akwai bambanci a tsakanin tsohon shirin da kuma sabon, ya kara da cewa yanzu an shiga sabon babi inda ake sa ran gudanar da wani zabe na raba gardama, sai dai a wannan karon babu wani dalili na kin amincewa 'yan majalisar na yanke dangantaka da EU a cewarsa.

A ranar ashirin da tara ga watan Maris na wannan shekarar ta 2019, Birtaniya ke fatan ganin ta fice baki daya daga Tarayyar Turai sai ana baiyana shakku kan hakan ganin irin tirjiyar da ta fuskanta tun daga farkon shigar da kudirin.