Britaniya: Ba alamun ficewa daga Kungiyar EU
September 9, 2019Talla
Yanzu da wannan amincewar, yunkurin Firai minista Boris Johnson na fitar da kasar a ranar talatin da daya ga watan Oktoba ya fuskanci cikas. An sami nasarar yin hakan bayan da majalisun kasar suka amince da kudurin.
A daya bangaren kuwa, kakakin majalisar John Bercow, ya ce zai yi murabus a ranar da wa'adin ficewar ke cika muddun aka sami kai a wani yanayi na ba-zata da zai saka 'yan majalisa bai wa Johnson goyon bayan gudanar da zaben gaba da cikar wa'adi ko kuma 'Snap election' a Turance. An dai dade ana kai ruwa rana kan zabin Britaniya na raba gari da kungiyar tarayyara Turai, lamarin da ya janyo rabuwa kanu da hargitsi a tsakanin jam'iyyun kasar.