Brazil za ta bada gudunmawa kan rage dumamar yanayi a duniya. | Labarai | DW | 27.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Brazil za ta bada gudunmawa kan rage dumamar yanayi a duniya.

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta bayyana cewar kasar ta za ta rage adadin iskar gas din da take futarwa da kashi 37 cikin dari nan da shekaru goma masu zuwa .

Shugaba Dilma Roussef dai na wadanan kalaman ne a yayin taron wuni uku na shugabanin duniya a majalisar dinkin duniya dake gudana a Amirka, a inda ta kara da cewar ya zama wajibi a kai ga sanya hannu a tsakanin shugabanin duniya don cimma yarjejeniyar sauyin yanayi da aka shirya gudanarwa nan da karshen wannan shekarar a birnin Paris.

Shugabar tace Brazil ta sanyawa kanta wa'adi na rage yawan adadin iskar gas din da take futarwa ne tare kara kashi 43 cikin dari nan da shekara ta 2030 wanda ke zama wani muhimmin mataki na dai-dai ta sauyin yanayi a duniya.