Brazil: ′Yan sanda sun tsare tsohon shugaba Lula | Labarai | DW | 04.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Brazil: 'Yan sanda sun tsare tsohon shugaba Lula

Rahotanni na nuni da cewa hukumar 'yan sanda ta tsare tsohon shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva inda take yi masa tambayoyi kan zargin cin hanci da rashawa.

'Yan sanda sun dakatar da tsohon shugaban kasar ta Brazil ne,biyo bayan wani bincike da suka gudanar a wannan Jumma'a a gidansa na birnin Sao Paulo da a gidajen abokanin aikinsa da ma sauran danginsa.

Babban mai shigar da kara na gwamnatin kasar ta Brazil Carlos Fernando dos Santos Lima wanda ke kula da aikin binciken ya ce suna zargin tsohon shugaban da iyalansa da karbar cin hanci na miliyan takwas na dalar Amirka a badakalar kamfanin Petrobras.