1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakile aikin masu tarzoma a Brazil

Yusuf Bala Nayaya MNA
January 6, 2019

A Brazil an jibge dakarun 'yan sanda a jihar Ceara da ke yankin Arewa maso Gabashi a kokari na daklile aiyukan tarzoma na kungiyoyin masu aikata miyagun laifuka da ke afka wa bankuna da motoci da shaguna.

https://p.dw.com/p/3B5PF
Brasilien Rio Polizei-Operation
Hoto: picture-alliance/AP Images/S. Izquierdo

Kusan 'yan sanda 300 ne aka jibge a birnin Fortaleza da ke zama babban birnin jihar ta Ceara da wasu birane sama da goma, ganin yadda a tsawon kwanaki hudu ake ganin kone-kone da lalata kadarorin gwamnati kamar yadda sakataren yada labaran gwamnatin kasar ta Brazil Guilherme Teophilo ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Agencia Brasil.

Yayin da ake bincike kan musabbabi na ta da hargitsin wasu rahotanni dai sun nunar da cewa cikin dalilai na ta da hargitsin har da batun kara tsaurara matakai na tsaro a gidajen kaso na kasar. Wannan dai na zama gwaji na kamun ludayi ga sabon shugaban kasar Jair Bolsonaro da aka rantsar a ranar Talatar da ta gabata.