1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magoya bayan Bolsonaro na ta da kura

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
January 9, 2023

Hukumomin shari'a a Brazil sun kaddamar da bincike, domin gano wadanda ke da hannu a kutse da magoya bayan tsohon shugaban kasa Jair Bolsonaro suka yi a majalisar dokoki da sauran gine-ginen gwamnati.

https://p.dw.com/p/4LvOw
Brazil | Brasilia | Shugaban Kasa | Lula da Silva | Palácio do Planalto
Shugaban Brazil Lula da Silva ya kai ziyara domin ganin barnar masu zanga-zangaHoto: Eraldo Peres/AP Photo/picture alliance

Bayan shafe sa'o'i da dama cikin wani abu mai kama da mamayar da aka yi a zauren majalisar Amirka da ke birnin Washington shekaru biyu da suka gabata, jami'an tsaro sun sake karbe ikon fadar shugaban kasa da majalisar dokoki da kotun kolin kasar Brazil. Daruruwan masu zanga-zangar adawa da mulki Shugaba Lula da Silva ne dai, suka mamaye gine-ginen a Lahadin karshen mako. A lokacin da ya yi bayani a birnin Brasilia, ministan shari'a da tsaro Flavio Dino ya bayyana cewar an fara gano wadanda suka lalata kadarorin gwamnati a Brasilia kuma doka za ta hukunta su. A halin yanzu dai fiye da mutane 300 ne aka kama, kuma ofishin mai shigar da kara ya bukaci da a a gaggauta gudanar da bincike domin tabbatar da "hukunta wadanda ke da hannu" a kutsen da aka kai kan gine-ginen hukuma. Hukumomi dai sun yi kokarin killace gine-ginen da kutsen ya shafa, amma duk da haka magoya bayan tsohon shugaban Brazil din Jair Bolsonaro sanye da riga ruwan goro sun yi nasarar kutsawa tare da yin mummunar barna har ma da lalata hatunan zane-zanen alfarma masu tarin yawa.

Brazil | Brasilia | Jair Bolsonaro | Lula da Siva
Magoya bayan tsohon shugaban Brazil sun yi ta'adi a gine-ginen hukumaHoto: Adriano Machado/REUTERS

Sannan an kuma yada faifan bidiyo a shafukan sada zumunta na zamani da ke nuna yadda aka lalata ofisoshin 'yan majalisa da hotunan wani mai zanga-zanga da ya zauna a kan kujerar shugaban majalisar dattawa, lamarin da ya yi kama da tayar da kayar baya na magoya bayan tsohon shugaban kasar Amirka Donald Trump a lokacin da suka mamaye Capitol shekaru biyu da suka gabata. Wata kungiyar 'yan jarida ta ruwaito harin da aka kai kan 'yan jarida biyar, inda aka  yi wa wani mai daukar hoto na kamfanin dillancin labaaran Faransa na AFP duka tare da sace masa dukkan kayan aikinsa.Tsohon shugaban Brazil Jair Bolsonaro wanda yake Amirka yanzu haka ya yi amfani da jerin  sakonnin Twitter wajen yin tir da abin da ya faru, inda ya danganta kutsen gine-ginen gwamnati da rashin hankali. Amma kuma ya yi watsi da zarge-zargen da magajinsa ya yi, inda ya ce ba su da hujjar cewa ya karfafa tashin hankali. Bolsonaro dai, ya bar kasar Brazil  kwanaki biyu gabanin rantsar da Lula tare da kin mika ragamar shugabancin kasar ga mutumin da ya kayar da shi a zaben watan Oktoba.

Brazi| Brasilia | Zanga-Zanga | Planalto Palast
Masu zanga-zanag sun yi kutse a majalisar dokokin Brazil domin nuna adawa da LulaHoto: Eraldo Peres/AP Photo/picture alliance

Da yawa daga cikin abokan Bolsonaro sun nisanta kansu daga kutsen na ranar Lahadi, ciki har da Valdemar Costa Neto shugaban jam'iyyarsa ta Liberal Party (PL) wanda ya ce "ranar bakin ciki ce ga al'ummar Brazil".Shi ma gwamnan jihar Brasilia Ibaneis Rocha da ke zama amini ga Bolsonaro ya nemi afuwar Shugaba Lula a wani faifan bidiyo, inda ya danganta wadanda suka lalata gine-ginen da 'yan ta'adda. Wannan kutse na gine-ginen gwamnatin Brazil ya haifar da tofin Allah tsine a duniya, inda shugaban Faransa Emmanuel Macron ya shaida wa Lula cewa yana da goyon bayan Faransa 100 bisa 100. Shi kuwa takwaransa na Amirka Joe Biden ya dauki tashin hankalin a matsayin abin kunya, yayin da shugaban Mexico Andrés Manuel Lopez Obrador ya yi tir da abin da ya kira "yunkurin juyin mulkin 'yan mazan jiya a Brazil". Tun bayan da Bolsonaro ya fadi zabe ne magoya bayansa suka fara gudanar da zanga-zanga a gaban barikin sojoji, domin neman su shiga tsakani su hana Lula komawa kan karagar mulki.