1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brazil: Gobara a filin wasa na Flamengo

Ahmed Salisu
February 8, 2019

Tashin wata gobara a filin wasa na matasan 'yan kungiyar kwallon kafar Flamengo da ke Brazil ta yi sanadiyyar rasuwa mutane 10 yayin da wasu guda uku suka samu munanan raunuka.

https://p.dw.com/p/3D0iL
Paris Wohnhausbrand,
Hoto: picture-alliance/AP/Feuerwehr Paris

Jami'an kashe gobara da suka yi aikin wajen kashe gobarar suka ce wutar ta tashi ne da sanyin safiya kuma ya zuwa yanzu ba a kai ga gano abin da ya haifar da tashin wutar ba. Tuni dai magoya bayan kungiyar da 'yan uwa da abokan arzikin wanda suka rasu a gobarar suka shiga yanayi na zaman makoki. Ya zuwa yanzu dai kungiyar ba ta kai ga cewa komai ba game da wannan lamari. Kungiyar ta Flamengo dai na daga cikin fitattun kungiyoyin kwallon kafa a kasar ta Brasil.