Borussia Dortmund na ci gaba da jan zare | Zamantakewa | DW | 03.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Borussia Dortmund na ci gaba da jan zare

A gasar Bundesliga kungiyar Borussia Dortmund na ci gaba da jan zarenta a saman tebir. Yayin da Najeriya ta lashe kofin kwallon kafa na Afirka na mata karo na 13 da aka buga a kasar Ghana.

A wasannin kwallon kafar Jamus na Bundesliga inda a karshen mako aka buga wasannin mako na 13 inda tauraran yaya karama wato kungiyar Dortmund ke ci gaba da haskakawa a kakar wasannin shekarar bana inda ta jera wasanni 13 ba tare da tabaras da koda daya ba ya zuwa yanzu. A ranar Asabar da ta gabata bayan da ta karbi bakuncin kungiyar Freiburg a filin wasa na Signal Iduna Park a gaban 'yan kallo kimanin dubu 80 ta ko lallasa ta da ci biyu da babu. Dan wasanta na gaba dan asalin kasar Spain Paco Alcacer wanda alkalumman Bundesligar suka nunar da cewa yana cin kwallo daya a kowadanne mintoci 29 a wannan karo ma ya cika sunnar tasa inda ya zura kwallon karshe ta kungiyarsa a daidai lokacin da aka shiga karin lokaci na kammala wasan.

Har yanzu kan batun kwallon kafar amma a wannan karo a nahiyar Afirka inda bayan da hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF ta janye wa Kamaru nauyin shirya gasar cin kofin kwallon kafar Afirka ta 2019 aka shiga cikin halin kila-wakala na shirya gasar a shekara mai kamawa. Ya zuwa yanzu dai hankali ya karkata ga kasashen Afirka ta Kudu da Maroko wadanda ke da wadatattun filayen wasa da ma Hotel na iya karbar bakuncin wasan a cikin takaitaccen lokaci. A na sa ran dai samun amsar daya daga cikin kasashen a wannan mako.

FBL-CAMEROON-CAF (AFP/Getty Images/R. Kaze)

Kamaru dai daukar gasar ta CAF ya gagara

A dai dai lokacin da ake cikin halin kila-wakala a game da gasar cin kofin kwallon kafar ta Afirka a shekara mai kamwa, a jiya Lahadi an kammala gasar cin kofin kwallon kafar Afirkar ta mata karo na 13 da ta gudana a kasar Ghana, Kuma Najeriya wacce da ma ta dauki kofin son 11 a baya ita ce ta sake lashe shi a wannan karo bayan da ta lallasa kasar Afirka ta Kudu a karawar karshe.

Bari mu karkare shirin namu da Damben zamani inda zakaren duniya na masu nauyi Deontay Wilder dan Amirka mai shekaru 33 ya yi nasarar ci gaba da rikon kambunsa bayan da suka kara da Tyson Fury dan Birtaniya mai shekaru 30 a karawar da suka yi a cikin daren Asabar a birnin Los Angeles a gaban 'yan kallon dubu 18. 'Yan damben biyu dai sun yi wa juna alwashin sake gobzawa a shekara mai zuwa.

Sauti da bidiyo akan labarin