Borno: Samar wa mata audugar al′ada kyauta | Himma dai Matasa | DW | 02.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Borno: Samar wa mata audugar al'ada kyauta

A’ishatu Kabu Damboa wata matashiya ce da ta rungumi aikin samar da audugar mata ta jinin al’ada ga ‘yan mata da ba su da hali a sansanin ‘yan gudun hijra da kuma makarantu a shiyyar Arewa maso Gabshin Najeriya

Ba kasafai ake samun mata na fitowa fili su na magana a kan abinda ya shafi al'adar su ta jinin haila ko kuma wani abu da ya kebantu ne ga mata su kadai ba abinda ake ganin hakan na cutar da mata ko kuma jefa cikin kunci da ka iya shafar rayuwar su baki daya.

Jinin al'ada ko kuma haila na daga cikin abubuwan ake boye yin magana a kai in dai ba tsakanin jinsi daya wato ko dai mata zallansu ko kuma maza zalla inda mata da dama ke cutuwa a lokacin da su ka fara jinin al'ada saboda jahiltar abinda ya kamata su yi.

Wannan ne ya sa A'ishatu Alh Kabu Damboa wace ta ke shirin kamala karatun ta na jami'a a fannin koyon aikin Jarida ta zabi fotowa domin fadakar da mata har ma da maza muhimmancin taimakawa mata wajen basu audugar da za su ke amfanin da ita a lokacin da su ke al'ada.

Daruruwan mata sun samu cutuka saboda amfani da wasu tsummokara ko kuma wasu abubuwa marassa tsabta wajen tare jinin Al'ada saboda rashin kudin sayen auduga ta zamani ko kuma rashin sainta.

A'ishatu Alh Kabu Damboa wacce gudun hijira ya kawo ta Maiduguri ta na amfani da hanyoyin sadarwar zamani wajen neman tallafi na sayen audugar mata inda ta ke rabawa ‘yan mata a sasanonin ‘yan gudun hijira da kuma makarantun sakandare.