1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Bama-bamai sun halaka yara a Afghanistan

April 2, 2022

Ba dai sabon abu ba ne, kananan yara su yi wasa da bom din da bai kai ga fashewa ba a Afghanistan, a sakamakon yadda aka kwashe tsawon lokaci kasar na cikin tashin hankali. 

https://p.dw.com/p/49N1K
Afghanistan | Bombenexplosion in Herat
Hoto: Mohsen Karimi/AFP

Kimanin yara guda biyar sun rasa rayukansu a sakamakon wasu ababen fashewa da suka tarwatse a wurare biyu a birnin Herat na Afghanistan. Rahotannin da DW ta samu na cewa akwai wasu mutane 20 da ababen fashewar suka jikkata. 

Hukumomin Taliban masu mulkin Afghanistan sun ce lamarin ya faru ne a ranar Jumma'a, lokacin da kananan yara suka tono ababen fashewar, suka fara wasa da su.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin d'ana bama-baman. Sai dai Taliban ta ce ta yi nasarar tono wasu karin bama-bamai guda biyu da ba su kai ga fashewa ba a kusa da in da lamarin ya faru a ranar Jumma'a.