1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bolsonaro na jan kafar amsa shan kaye

November 1, 2022

Shugaba Jair Bolsonaro na Brazil na jan kafar amincewa da shan kaye a zaben shugaban kasa wanda tsohon shugaba Lula Da Silva ya lashe.

https://p.dw.com/p/4IuZ4
Shugaba Jair Bolsonaro na Brazil
Shugaba Jair Bolsonaro na BrazilHoto: EVARISTO SA/AFP/Getty Images

Direbobin manyan motoci na Trailer da ke goyon bayan shugaban Brazil mai barin gado Jair Bolsonaro sun toshe hanyoyi dabam-dabam a jihohi 20 na kasar a wani mataki na adawa da rashin nasarar da Bolsonaro ya fuskanta a zaben shugaban kasa.

Wasu hotunan bidiyo na direbobin da ke yawo a shafukan sada zumunta na nuna yadda suka toshe manyan hanyoyin kasar tare da kira ga sojojin Brazil da su yi juyin mulki domin hana zababben shugaba Lula da Silva da ya yi nasara a zaben karbar mulkin kasar.

Wannan na zuwa ne a yayin da kasar ta shiga cikin zaman zulumi sakamakon shirun da Shugaba Bolsonaro ya yi kwana guda bayan bayyana sakamakon zaben na ranar Lahadin da ta gabata. To sai dai wasu makusantan shugaban sun ce ana sa ran zai fadi matsayarsa ta karba ko watsi da sakamakon zaben a wannan Talata.