Boko Haram ta kwace garin Kerawa na Kamaru | Labarai | DW | 23.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta kwace garin Kerawa na Kamaru

Sojin Kamaru sun kama hanya zuwa kwato garin Kerawa da ke Arewacin kasar bayan da ya fada hannun mayakan kungiyar tsageru ta Boko Haram a wannan Jumma'ar.

Kungiyar Boko Haram ta yi nasarar kwace birnin Kerawa na yankin Arewa mai nisa na kasar Kamaru mai kunshe da mutane dubu 50. Wata majiyar hukumomin yankin Arewa mai nisa na kasar ta kamaru ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa harin ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar a gidan radiyo na kasa ministan hatsa labarai kana kakakin gwamnatin kasar ta kamaru ya ce babu koda mita daya na fadin kasar da ya fada a hannun wadanda ya kira tsageru.

Amma kuma wasu rahotanni daga kasar ta kamaru na cewa yanzu haka daruruwan sojojin kasar dauke da manyan makamai yaki sun kama hanyar zuwa neman kwato birnin daga hannun mayakan Kungiyar ta Boko haram.

Kama wannan birni na kasar kamaru wanda shi ne na farko da Boko Haram din ta yi a cikin watannin baya bayan nan ya zo ne kasa da mako daya da kasar Amirka ta kai sojojinta 300 da jiragen yaki da nufin yaki da Kungiyar ta boko Haram