Boko haram ta kashe mutane 15 a Kautikari | Labarai | DW | 30.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko haram ta kashe mutane 15 a Kautikari

Wani harin da masu gaggwarmaya da makamai suka kai yankin Arewa maso gabashin Najeriya ne ummal aba'isan salwantar rayukan fararen Hula a garin Kautikari.

Wasu 'yan bindiga da ake dangantawa da 'yan Boko Haram sun yi luguden wuta a garin Kautikari na jihar Bornon Najeriya inda suka kashe akalla mutane 15 dukkaninsu fararen hula. Jami'an tsaro da kuma wadanda suka shaidar da lamarin sun bayyana cewar harin ya auku ne a dare Litinin zuwa wannan Talatar a tazarar kilometa goma da garin Chibok inda aka sace 'yan matan nan 'yan makaranta sama da 200 a watan Afirilun da ya gabata.

Ita dai kungiyar Boko Haram dake gaggwarmaya da makamai da ta yi ikirarin kafa daula ta musulunci, ta sake sace mata da kananan yara 135 a farkon wannan wata na Disemba, tare da kashe wasu karin 35 a yankin Arewa maso gabashin Najeriyar.

Sama da mutane 10 300 ne dai suka rasa rayukansu a yankin Arewa maso gabashin Najeriya a cikin wannan shekarar da muke ciki sakamakon hare-haren da kungiyar da aka fi sani da Boko Hara ke kaiwa. Hakazalika fiye da mutane miliyan daya ne suka kaurace wa matsugunansu tun bayan da hare-hare suka zama ruwan dare a wannan kasa.