Boko Haram ta karbe wasu sassan Borno | Siyasa | DW | 21.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Boko Haram ta karbe wasu sassan Borno

Kungiyar Boko Haram ce ke da ikon sassan arewaci da tsakiyar jihar Borno duk da barazanar gwamnatin kasar na hukunta duk wanda ya yi ikirarin iko da wani bangare.

Rahotanni na nuna cewa kungiyar Boko Haram ita ce yanzu haka ke rike da ikon sassan yankin arewaci da kuma tsakiyar jihar Borno, duk da gargadi da gwamnatin ta yi na cewa dakarun kasar za su dauki matakin da ya dace bayan da bayanai suka tabbatar da kungiyar ta kafa tutocin ta a garin Damboa a karshen makon nan.

Banda garin Damboa akwai garuruwa da dama da kungiyar ta kafa tutocinta a sassan arewaci da tsakiyar jihar tare da kafa shingen bincike na ababan hawa don tantance masu bin hanyoyin.

Direbobi da matafiya sun bayyana cewa bin hanyoyin da suka ratsa wannan yankuna na da matukar hadari saboda yadda ‘yan bindigar suka killace hanyoyin kuma babu wani mataki da jami'an tsaro na gwamnati ke yi dangane da wannan lamari.

Nigeria Anschlag in Abuja 25.06.2014

Hare-haren Boko Haram sun yi sanadin mutuwar mutane da dama

Wasu rahotanni sun nuna cewa yayin tantance masu wucewa ‘yan bindigar kan hallaka wasu ko kuma yin awon gaba da wasu tare da kwace kayan abinci da manyan motoci ke safarar su zuwa ciki ko wajen Najeriya.

Wani bawan Allah da ya bar garin Damboa ranar Lahadin nan da yamma wanda ya isa garin Biu ya shaida wakilin DW halin da ya bar garin a tattaunawar da ya yi da shi ta wayar tarho.

Ya ce"wasu da suka tsira daga hare-haren wanda yanzu haka suka isa Maiduguri sun bayyana ta wayar tarho cewa suna cikin ukuba inda masu ‘yan uwa suka samu wuri, sauran kuma suka fake ko dai a karkashin bishiya ko kuma a makarantun firamare suna samun taimako daga al'ummar garin"

Hanyoyin da suka fi fuskantar wannan hadari yanzu haka sun hada da hanyar da ta tashi daga Maiduguri zuwa Gamboru, wacce take danganawa da kasar Kamaru da hanyar Maiduguri zuwa Biu zuwa Gombe da hanyar Maiduguri zuwa Bama da Gwoza.

Direbobi da sauran matafiya sun kauracewa wadan nan hanyoyin inda babbar hanyar daya tilo da ta yi saura mai shiga Maiduguri itace wacce ta tashi daga Potiskum zuwa Damaturu zuwa Maiduguri.

Nigeria Soldaten

Rundunar sojan Najeriya na kokarin karya kashin bayan Boko Haram

Dan majalisar dokoki mai wakiltar yankin Gamboru –Ngala a majalisar dokokin jihar Borno Hon. Idrissa Jidda ya tabbatar wa manema labarai killace hanyoyin.

Tuni dai gwamnatin tarayyar Najeriya ta mayar da martani kan wadannan rahotannin da ke cewa 'yan Boko Haram sun kwace wasu yankuna, musamman ma rahoton garin Damboa wanda aka ce sun kafa tutarsu a can.

Gwamnatin Najeriya ta bakin Mista Mike Omeri shugaban cibiyar samar da bayanai kan yaki da ta'addanci a kasar yace "matukar wadannan bayanai suka tabbata gaskiya ne to kuwa dakarun kasar za su dauki matakin da ya dace na kwato wadan nan yankuna daga hannun ‘yan Boko Haram"

Yanzu haka bayanai da suke fitowa sun nuna cewa Jami'an tsaro da kuma matasan nan dake taimakawa jami'an tsaro da aka fi sani da Civilian JTF sun bazama zuwa yankin garin Damboa da nufin kwato garin daga dakarun kungiyar.

Mawallafi: Al-Amin Suleiman Mohammad
Edita : Yusuf Bala

Sauti da bidiyo akan labarin