Boko Haram ta kai sabon hari a Najeriya | Labarai | DW | 01.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta kai sabon hari a Najeriya

Rahotanni daga Najeriya sun tabbatar da wani hari da mayakan Boko Haram suka kai a yankin tafkin Chadi inda aka yi asarar rayuka. Lamarin dai ya shafi jami'an tsaro.

Wani fada da ya barke tsakanin sojoji da mayakan kungiyar Boko Haram da ke da alaka da IS a yankin arewa maso gabashin Najeriya ya yi sanadiyar mutuwar sojoji 25 da kuma a kalla mayakan na Boko haram 40. 


Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewar wani kwamandan soji da ke a yankin ya ce mayakan na bangaren ISWAP sun kai harin ne a wani barikin soji da ke garin Baga a gabar tafkin Chadi inda gumurzu ya yi sanadin asarar rayuka daga bangarorin biyu.