Boko Haram ta hallaka wasu sojojin Najeriya | Labarai | DW | 11.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta hallaka wasu sojojin Najeriya

Kungiyar Boko Haram reshen ISWAP mai ikrarin jihadi a yammacin Afirka ta kaddamar da wani harin kwantar bauna kan ayarin sojijin Najeriya a jihar Borno tare da hallaka da dama baya ga raunata wasu.

A yankin Arewa maso gabashin Najeriya sojoji da dama ne suka gamu da ajalinsu a yayin wani kwantar bauna da mayakan kungiyar Boko Haram reshen ISWAP suka yi kan wani ayarin sojin Najeriya da ke kan hanyarsu ta zuwa garin Gudumbali a gabashin jihar Borno.

Masu aiko da rahotanni sun bayyana cewa, Najeriya ta yi hasarar sojojinta da dama, tare da jikkatar wasu, baya ga dumbin hasarar makamai da motocin yaki da sojojin suka yi a yayin harin na 'yan Boko Haram.

A nata bangare kungiyar ISWAP mai ikrarin jihadi a yammacin Afirka ta sanar da daukar alhakin harin, tana mai cewa ta hallaka sojoji da dama.