Boko Haram ta farwa masu zabe
March 28, 2015Talla
Rahotanni daga Najeriya, na cewa 'yan bindiga da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun afkawa runfunan zabe a wasu yankunan arewa maso gabashin kasar.
Bayanai sun ce maharan sun buda wuta a kan masu zabe a kauyukan Birin Bolawa da kuma Birin Fulani da ke yankin Nafada a jihar Gombe inda suka kashe akalla mutane biyu.
Wani jami'in zabe da bai so a bayyana sunansa ba, ya shaidawa kamfanin labaran Faransa AFP cewa, sun yiwo 'yan bindigan na cewa ''ai mun riga mun gargade ku kan zabe''.
Cikin wani faifan bidiyo a watan jiya, shugaban mayakan Boko Haram Abubakar Shekau, ya yi barazanar kawo tsaiko ga zabukan na Najeriya.