Boko Haram na fafatawa da sojoji a garin Bama | Labarai | DW | 01.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram na fafatawa da sojoji a garin Bama

Rahotanni da ke fitowa daga jihar Borno na nuna cewa rundunar Sojojin Najeriya ta yi nasarar korar 'yan bindiga da suka afkawa garin Bama da sanyin safiyar yau Litinin

Wasu da suka shaida abin da ya wakana, sun bayyana wa wakilin mu a Gombe Amin Suleiman Mohammed ta wayar tarho cewa, ‘yan bindigar sun shiga garin ne da misalin karfe hudu na asubahi, inda suka afkawa garin tare da harbin kan mai uwa da wabi, abun da ya tilastawa mutane garin ficewa don tsira da rayukan su.

Wata rundunar sojoji a Maiduguri da ta isa wurin, ta samu nasarar dakile kokarin karbe wannan gari. Sai dai har yanzu ba'a san adadin wadanda abin ya rutsa da su ba, inda babu wani bayani da ya fito daga hukumomi ko jami'an tsaron Najeriya kan wannan farmaki na garin Bama dake a nisan kilomita 80 da Maiduguri fadar gwamnatin jihar ta Borno.

Mawallafi: Salissou Boukari

Edita : Usman Shehu Usman