Boko Haram: An zargi Najeriya da gazawa | Labarai | DW | 24.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram: An zargi Najeriya da gazawa

Al'ummar da ke arewa maso gabashin Najeriya sun koka kan abinda suka kira gazawar gwamnatin kasar wajen kare su daga hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram.

Mazauna yankin da suka tattauna da tashar DW suka ce mahukunatan kasar sun fi maida hankali ne ga zabukan 2015 da ke tafe maimakon tsare lafiyarsu da kare dukiyoyinsu.

Wannan yanayi ne ma ya sanya al'ummar Musulmi da na Kirista da ke zaune a yankunan da abin ya shafa suka yanke hukuncin kare kawunansu da wuraren ibadunsu kamar yadda wani shugaban al'umma Alhaji Ali Sokoto ya shaida.

Rikicin Boko Haram a Najeriya dai ya yi sanadin rasuwar dubban mutune baya ga raba wasu da matsungunansu da ma jawo asara ta dukiya.