Bobi Wine ya yi fatali da sakamakon zabe | Labarai | DW | 17.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bobi Wine ya yi fatali da sakamakon zabe

Jami'yyar adawa a kasar Yuganda ta yi fatali da sakamakon zaben shugaban kasar da aka sanar a hukumance wanda ta ce ya na ciki da kurakurai da ma aringizon kuri'u.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da nasarar shugaba Yoweri Museveni a matsayin wanda ya lashe zaben da kaso 58.6 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Jam'iyyar adawa ta National Unity Party (NUP) ta Bobi Wine, ta yi kira ga mahukunta da su sakar musu dan takarar su wanda daruruwan sojoji suke tsare da shi a cikin gidansa tare da iyalansa da ma cin zarafin magoya bayansa.

Tuni da jam'iyyar ta NUP ta yi kira ga al'ummar kasar da su kauracewa wannan sakamakon. Haka zalika ta kara jadda manufarta na ci gaba da kwato kasar daga hannun mulki na kama karya a cewar sanarwar da ta fidda.