Bob Dylan ya lashe kyautar Nobel ta adabi | Labarai | DW | 13.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bob Dylan ya lashe kyautar Nobel ta adabi

Bob Dylan shahararren mawaki dan kasar Amirka ya lashe kyauta Nobel ta adabi ta shekarar bana a sakamakon gudunmawar da ya bada wajen raya wakokin gargajiya na Amirkawa.

An bai wa Bob Dylan wani shahararren mawaki na kasar Amirka kyautar Nobel ta adabi ta wannan shekara ta 2016. Wannan dai shi ne karo na farko da wani mawaki ya taba samun wannan kyauta ta Naobel ta Adabi. Mahalartar bikin bayar da kyautar da ya gudana a wannan Alhamis a birnin Stockholm, sun bayyana gamsuwarsu da bai wa Bob Dylan wannan kyauta wacce ga al'ada ake bayar da ita ga mutanen da suka yi fice wajen rubuta littafan adabi. 

Sara Danius babbar magatakardar cibiyar kwararru a fannin adabi ta Academie ta ce Bob Dylan dan shekaru 75 a duniya ya samu kyautar ne a sakamakon  kokarin da ya yi wajen raya wakokin gargajiya na Amirka a cikin salon magana da rubuto na kafiya.