1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Blinken na matsa wa Isra'ila lamba don tsagaita wuta a Gaza

Mouhamadou Awal Balarabe
March 22, 2024

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya jaddada wa Isra'ila bukatar kai karin kayan agaji a Zirin Gaza, a daidai lokacin da kwamitin sulhu na MDD ke gabatar da kuduri na tsagaita bude wuta a yankin Falasdinu.

https://p.dw.com/p/4e1CV
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a lokacin da ya isa Isra'ila
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a lokacin da ya isa Isra'ilaHoto: Evelyn Hockstein/REUTERS

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa birnin Tel Aviv na kasarIsra'iladomin jaddada bukatar kai karin agajin jin kai ga Zirin Gaza, a daidai lokacin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke shirin gabatar da kuduri na tsagaita bude wuta a yankin na Falasdinu.  Fadar mulki ta Washington na neman shawo kan kawayarta Isra'ila don ta kauce ma kai farmaki ta kasa kan garin Rafah da ake fargabar karuwar 'yunwa tsakanin fararen hula.

Karin bayani: Duniya na muradin kafa kasar Falasdinu

Kasar Burtaniya da ke zama mamba ta dindindin a kwamitin sulhu da kuma Ostareliya sun yi kira da a gaggauta kawo karshen yakin da aka shafe watanni biyar da rabi ana yi a zirinGaza, domin ba da damar isar da kayan agaji da kuma sako 'yanIsra'ila da ke hannu Hamas tun bayan mummunan harin 7 ga watan Oktoba. Sai dai a  yayin da jami'an diflomasiyya ke ci gaba da matsin lamba, ana ci gaba da gwabza fada a ciki da wajen asibitin al-Chifa, inda sojojin Isra'ila suka yi ikirarin kashe Falasdinawa sama da 150.