Blaise Campaore ya ga uwar bari kan ta-zarce | Siyasa | DW | 30.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Blaise Campaore ya ga uwar bari kan ta-zarce

Bayan boren yan kasar, gwamnatin Burkina Faso ta yi amai ta lashe inda ta bada sanarwar janye bukatar yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar

Biyo kona majalisar dokoki inda nan ne za a kada kuri'ar yin gyaran fuskar ga kundin tsarin mulkin, masu zanga-zangar suka fantsama a fadar shugaban kasa, inda suka yi ta dauki ba dadi da jami an tsaro dake gadin fadar, wasu rahotannin sunce an kona gidan kanin shugaba Blaise Campaore, wato Farancois Campaore. Ministan sadarwa Alain Edouard kuma kakakin gwamnatin Burkina Faso da DW ta tuntube shi kan halinda ake ciki, sai ya bayyana mana cewa bai iya magana damu a lokacin.

Sanarwar da dakarun kasar suka bayar na cewa suna tare da masu zanga-zangar na nuni da cewa wani shafin tarihi ne ke shirin juyawa, duk da cewa Gwamnatin Blaise Campaore ta bada sanarwar janye wannan bukata tayin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki, masu zanga-zangar sun fantsama a fadar shugaban kasar, bayan kona majalisar dokoki. Inda nan ne za a kada kuri'ar yin gyaran fuskar ga kundin tsarin mulkin. Masu zanga-zangar da suka fantsama a fadar shugaban kasa, sun yi ta dauki ba dadi da jami an tsaro dake gadin fadar.


Sauti da bidiyo akan labarin