Birtaniya ta amince da ka′idojin EU | Labarai | DW | 04.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birtaniya ta amince da ka'idojin EU

Birtaniya da kungiyar Tarayyar Turai sun cimma matsaya kan wasu sharuda kan tattaunawar da za ta ba wa Birtaniya damar kammala shirin ficewa daga kungiyar EU.

Sai dai a yanzu Birtaniya ta amince da dukkanin sharuda kan iyakoki da take takaddama da makotanta, ciki har da batun sassauci tsakanin ta da lardin Ireland ta Arewa.

A baya Birtaniya ta amince da biyan kudi Euro biliyan 50 a wani yunkuri na mutunta sharuda da EU ta gindaya mata. Sai dai jami'an diplomasiyya na ganin rashin ba da hasken Birtaniyar kan 'yancin 'yan wasu kasashen Turai da ke zaune a kasar, na haifar da kokonto kan makomar cimma matsaya tsakaninta da kungiyar Tarayyar Turai da EU.

A yanzu haka Firaministan Birtaniya Theresa May ta bayyana kyakkayawan fata a tattaunawarta da shugaban majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk, inda take ganin tattaunawar za ta yi tasirin samun damar ci gaba da tattauna batun ficewarta daga kungiyar EU.