Birtaniya ta amince da dokar cinikayya da EU | Labarai | DW | 30.12.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birtaniya ta amince da dokar cinikayya da EU

Majalisar dokokin Birtaniya ta kada kuri'a da gagarumin rinjaye don amincewa da yarjejeniyar kasuwanci da Kungiyar Tarayyar Turai, abinda ya share fagen ficewar kasar daga kungiyar cikin tsari.

Yayin da ya rage yan kwanaki zuwa cikar wa'adin, yan majalisa 521 suka kada kuri'ar amincewa, 73 kuma suka ki amincewa. Yan majalisar masu rajin ballewar Birtaniyar sun baiyana matakin da cewa kasar ta kwato yancinta daga kungiyar tarayyar Turai.

Yayin da a nasu bangaren masu goyon bayan kasancewar Birtaniya a cikin kungiyar ta EU suka nuna takaici da rashin dunkulewar cinikayya da Birtaniya da ke zama babbar abokiyar huldar tattalin arziki.

Yarjejeniyar za ta zama doka da zarar yan majalisar dattijai sun bada sahalewa sannan ya sami tabarrakin sarauniya Elizabeth ta biyu.

A shekarar 2019 Birtaniya ta fice daga kungiyar amma ta cigaba da zama cikin kawancen tattalin arziki yayin da ake cigaba da tattaunawa, wa'adin da zai kare da karfe 11 na dare agogon London a ranar alhamis 31 ga watan Disamba.

Shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen da shugaban majalisar dokokin Turai Charles Michel sun rattaba hannu akan daftarin yarjejeniyar a wani kwarya kwaryar biki a birnin Brussels. An kuma gabatar da daftarin ga Firaministan Birtaniya Boris Johnson wanda shi ma ya rattaba hannu.