1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Theresa May ta sake shan kayi a majalisa

Yusuf Bala Nayaya
February 14, 2019

Kwanaki 43 kafin cikar wa'adi na fita daga EU kenan, wannan faduwa dai na nuni da cewa kusan firaministar ba ta da sauran goyon baya don sake tattaunawa da mahukuntan da ke a Brussels.

https://p.dw.com/p/3DPVg
Großbritannien London - Theresa May im House of Commons
Hoto: picture-alliance /Xinhua/UK ParliamentJ. Taylor

Firaministar Birtaniya Theresa May ta kara samun sanyin gwiwa bayan da ta sake shan kayi a gaban 'yan majalisar dokokin kasar. 'Yan majalisa 303 sun ki goyon baya yayin da 258 suka mara mata baya a bukatar gyara kan matsayarsu ta baya kafin a koma ga Kungiyar EU da ta ce babu batu na kwaskwarima a matsayarsu da Birtaniya.

An dai kada kuri'ar ne kan bukatar ganin firaministar ta sake komawa ga Kungiyar Tarayyar Turai don su daddale yarjejeniya ta karshe kan shirin fitar ta Birtaniya daga EU kwanaki 43 kafin cikar wa'adi. Wannan dai na nuni da cewa kusan firaministar ba ta da sauran goyon baya don sake tattaunawa da mahukuntan da ke a Brussels.

Tun da fari dai wasu 'yan majalisar dokokin Birtaniya daga bangaren masu ra'ayin mazan jiya da ke mulki wadanda kuma ke mara baya ga shirinta na fita daga Kungiyar Tarayyar Turai sun nunar da cewa za su kaurace wa kada kuri'a a wannan Alhamis, abin da ke zama na kaico ga Firaminista Theresa May adaidai lokacin da take neman goyon bayansu.