1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnati na fuskantar matsin lamba a Birtaniya

Zulaiha Abubakar MNA
September 12, 2019

Birtaniya ta bayyana hasashen karancin abinci da zanga-zangar da kasar za ta fuskanta idan ba a cika sharuddan kammala ficewa daga kungiyar EU ba, a matsayin abin da za a iya daukar matakin karewa a hukumance.

https://p.dw.com/p/3PU5o
Boris Johnson
Hoto: picture-alliance/ZumaPress/London News Pictures/G. Cracknell Wright

Wannan jawabi na fita ne bayan Firaminista Boris Johnson ya karyata zargin da al'umma suka yi masa na yaudarar sarauniya Elizabeth ta biyu kan dalilan dakatar da majalisar dokoki a lokacin da makwanni biyu suka rage kasar ta fice daga kungiyar EU.


A farkon hawansa mulki Firaminista Johnson ya dauki alwashin ganin kasar ta cika burinta na ficewa daga kungiyar tarayyar Turai a ranar 31 ga watan Oktobar bana.

Gwamnatin Birtaniya ta fidda bayanan matsalolin da kasar za ta fuskanta idan ta bar kungiyar ba tare da jarjejeniyar ficewa ba bayan matsin lamba daga zauren majalisar. A nata bangaren jam'iyyar adawa ta Labour ta bukaci dawowar zauren majalisar cikin gaggawa don sake yin duban wannan batu na yanayin da Birtraniyar za ta iya tsintar kanta a ciki.