Biratniya na son alaka da EU bayan Brexit
November 15, 2018Talla
Theresa May ta ce tsare-tsaren sun dauki matakai masu zafin gaske musamman kan abin da ya shafi matakan tsaro a kan iyakar Birtaniya da Irlan da kuma harkar kudi da zai rage wa Biratniya radadi bayan ballewa daga EU.
Duk da cewa firaministar ta fuskanci zazzafar adawa kan matakan nata a ciki da wajen jam'iyyar ta, amma ta jadada da cewa matakan ba su da illa ga Biratniya ba.